Bravo ya koma Manchester City
Pep Guardiola ya tabbatar dauko mai tsaron gidan Barcelona Claudio Bravo wanda kan hanyarsa ta zuwa Manchester City domin maye gurbin gwalkifan kungiyar Joe Hart.
Wallafawa ranar:
Tun bude wasannin Firimiya dai Guardiola ke aje Hart a benci . Kuma rahotanni sun ce Bravo ya nufi Ingila a yau Talata domin kammala cinikin shi akan kudi fam miliyan 17.
Wasu rahotanni daga Birtaniya sun ce ana diba lafiyar shi yanzu haka.
Guardiola dai ya soma aikin horar da Manchester City da kafar dama inda ya lashe dukkanin wasannin da ya buga a Firimiya Lig.
A ranar 10 ga Satumba ne dai Guardiola zai soma adawa da Mourinho inda za su kece raini a tsakanin Manchester United da Manchester City.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu