Isa ga babban shafi
Wasanni

An lalata mutum-mutumin Messi na Argentina

Wasu mutane sun lalata mutum-mutumi na gwarzon dan wasan Argentina da ke taka leda a Barcelona Lionel Messi a birnin Buenos Aires, in da suka raba shi gida biyu. 

Mutum-mutumin Messi da aka raba gida biyu a birnin Buenos Aires na Argentina
Mutum-mutumin Messi da aka raba gida biyu a birnin Buenos Aires na Argentina ca.sports
Talla

Masu aika-aikar sun kuma karya wuya da hannayen mutum-mutumin na gwarzon dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar.

A cikin watan Junin bara ne hukumomin kasar suka kafa mutum-mutumin bayan dan wasan ya gaza lashe gasar Copa America, abin da ya tilasta masa daukan matakin yin riyata daga buga wa kasarsa tamaula duk da dai daga bisani ya janye ritayar.

Hukumomin kasar sun ce, tuni aka fara gyaran mutum-mutumin wanda aka kera da tagulla.

Messi mai shekaru 29 na da magoya baya da ke nuna masa kauna a Argentina, sannan kuma akwai masu nuna masa akasin haka bayan sun zarge shi da rashin zage danse wajen buga wa kasarsa ta asali kwallon kafa kamar yadda ya ke nuna bajinta a  Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.