Tennis: An haramtawa Mitsuhashi wasa har abada
Hukumar lura da wasan kwallon Tennis ta Duniya, ta haramtawa Junn Mitsuhashi dan kasar Japan buga wasan har iyaka rayuwarsa, tare kuma da tilasta masa biyan tarar dala 50,000.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da wasan kwallon na Tennis, ta dauki tsattsauran matakin kan Mitsuhashi ne, bayan samunsa da laifin yunkuri na bada cin hanci don sauya sakamakon wasan da zai buga a shekara ta 2015, a wata gasa Tennis da ta gudana a kasar Afrika ta Kudu.
A waccan lokacin dai Mitsuhashi yayi tayin bai wa Joshua Chetty, dala 2000, ya kuma kara masa wani kudin daga bisani, idan har bashi dama ya samu nasara a kansa, tayin da Chetty ya yi watsi da shi, tare da gabatar da korafi gaban hukumar lura da wasan kwallon Tennis ta Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu