Zubawa Coutinho kudi fiye da kima yasamu janyewa - Barcelona
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ce janyewar da ta yi daga burinta na sayan dan wasa Philipe Coutinho daga Liverpool, ya biyo bayan tsabar farashin kudi euro miliyan 200 da kungiyar ta Liverpool ta nema kafin sai da mata dan wasan.
Wallafawa ranar:
Daya daga cikin daraktocin kungiyar Barcelona, Albert Soler, ya ce basu ji dadin rashin samun sayan Coutinho ba, wanda da babu shakkah zai karfafa cinikin sabbin 'yan wasan da suka sayo a kasuwar cinikayyar da aka rufe a Juma'ar da ta gabata.
Sabbin 'yan wasan da Barcelon ta sayo sun hada da Ousmane Dembele , Nelson Semedo, Gerard Deulofeu da kuma Paulinho.
A gefe guda kuma kungiyar PSG ta Faransa ta ce, rashin tuntubarta kan lokaci da Barcelona ta yi, shi ne ya kawo nakasu ka kokarin saida mata dan wasanta na gaba Angel Di Maria.
Sai dai wata majiya daga Barcelona ta rawaito cewar har yanzu kungiyar na cigaba da kokarin cimma burin sayan Coutinho, dan wasan da kocin Liverpool Jurgen Klopp ke jaddada cewa ba na sayarwa bane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu