Dole Tevez ya rage taiba ko mu sallame shi - Wu Jingui
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua dake China, Wu Xiaoh ya ce dan wasansu na Gaba Carlos Tevez ya gaza bugawa kungiyar wasa yadda ya kamata, a dai dai lokacin da kungiyar ta Shenghai Shenhua ke daf da fadawa ajin ‘yan dagaji.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tevez wanda tsohon dan wasan Manchester United da Juventus ne kafin komawa China, yana fuskantar suka daga daraktoci da kuma magoya bayan kungiyarsa da Shenghai, duba da cewa a kowane mako guda yana dafe albashin Fan dubu 615,000 a matsayin albashi, ba kuma tare da yana tabukawa kungiyar komai ba.
A halin yanzu kocin kungiyar ta Shenghua Wu Jingui ya gargadi Tevez da cewa mataki na farko ma tilas ne a rage taiba, domin a cewar Jingui hauhawa kamar farashi da Teves ke yi, yana taka rawa wajen gaza ciwa kungiyar kwallaye.
Tun bayan bude kakar wasa ta bana kwallaye uku kawai Tevez ya kankarowa Shenghai Shenhua, kwallo daya tilo kuma ta karshe ita ce wadda ya jefa a wasan da Shanghai SIPG ta lallasa su da kwallaye 6-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu