Isa ga babban shafi
Wasanni-Ingila

Rooney na neman komawa wasa a China

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wakilin Wayne Rooney na Manchester United, Paul Stretford yana kasar China, don tattaunawa da wasu kungiyoyi game da yiwuwar komawar Rooney wasa a daya daga cikin kungiyoyin kasar.

Wayne Rooney na kungiyar Manchester United.
Wayne Rooney na kungiyar Manchester United. Reuters/Darren Staples
Talla

Hakan dai na matsayin manuniyar cewa kocin Manchester United Jose Mounrinho yayi na’am da sallamar kaftin din mai shekaru 31.

A ranar 28 ga watan Fabarairu na wannan shekarar za’a rufe kasuwar cinikin yan wasa ta kasar China.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya bayyana cewa bashi da tabbacin Rooney zai cigaba da zama tare da su nan da makwanni masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.