Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyar Chelsea ta lashe gasar Premier - Mourinho

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya ce tuni kungiyar Chelsea ta samu nasarar lashe kofin gasar Premier na kakar wasa ta bana.

Mai horar da Manchester United, Jose Mourinho
Mai horar da Manchester United, Jose Mourinho Reuters / Eddie Keogh Livepic
Talla

Mourinho ya ce idan aka yi la’akari da tazarar maki 8 da ke tsakanin Chelsea da mai biye da ita wato Manchester City, yayinda ya rage wasanni 13 a karkare gasar, hakan zai bawa tawagar Antonio Conte damar kwantar da hankali, domin neman lashe kofin FA na dai kasar ta Ingila.

A farkon watan Maris mai zuwa Manchester United da Chelsea zasu fafata a wasan kusa da kusa dana karshe, wato quarter finals kenan a neman cin kofin FA.

Chelsea ta samu kaiwa matakin ne bayan lallasa takwararta ta Wolves ta 2-0, yayinda Manchester United ta samu nasara kan Blackburn da 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.