Isa ga babban shafi
Turai

Manchester United da Barcelona sun fi Madrid kudi

Manchester United ta sha gaban Real Madrid a jerin kungiyoyin da suka fi samun kudi a duniya a kakar da ta gabata. Wannan ne karon farko da United ta karbe matsayin daga Real Madrid a shekaru 11 .

Filin Old Trafford, na Manchester United
Filin Old Trafford, na Manchester United REUTERS
Talla

Sakamakon binciken wanda Kamfanin Deloitte ya gudanar ya ce Manchester ta samu kudaden shiga ne da suka kai yuro miliyan 689 tsakanin kakar 2015 zuwa 16.

Yanzu Barcelona ce a matsayi na biyu, Real Madrid kuma ta dawo na uku ne a jerin kungiyoyin da suka fi kudi a bana.

Bayern Munich ce matsayi na hudu, sai Manchester City a matsayi na 5.

Sai dai kuma Barcelona da Real Madrid na iya karbe matsayin na farko a shekara mai zuwa saboda yadda Manchester United ba ta cikin kungiyoyin da ke buga gasar zakarun Turai a bana.

Jerin Kungiyoyin da suka fi kudi

A karon farko Kungiyoyin Firimiya ta Ingila guda 8 ne suka shiga jerin teburin attajiran kungiyoyin 20 wadanda suka samu kudi da suka kai euro miliyan 172.

Arsenal na matsayi na 7, Chelsea a mastayi na 8, Liverpool a matsayi na 9, Tottenham a matsayi na 12, West Ham United a mastayi na 18, sai Leicester City a matsayi na 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.