Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai horar da West Brom ya zargi Sanchez da aikata ha'inci

Mai horar da kungiyar West Brom Tony Pulis ya zargi dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez da aikata ha’inci ta hanyar faduwa da gangan a yadi na 18, ba tare da an yi masa mugunta ba.

Dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette a lokacin da yake murnar zura kwallo ta biyu a ragar West Brom.
Dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette a lokacin da yake murnar zura kwallo ta biyu a ragar West Brom. REUTERS/Dylan Martinez
Talla

A cewar Pulis kamata yayi a ce an hukunta Sanchez ta hanyar bas hi kati,saboda yunkurin aikata almundahanar.

Mai horar da kungiyar ta West Brom, ya kuma zargi alkalin wasa Bobby Madley, da shafawa idanunsa toka wajen hana kungiyar damar bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta samu, a lokacin da Mustafi na Arsenal ya tado dan wasansu Jay Rodriguez a yadi na Shatakwas.

Arsenal ce dai ta lallasa West Brom da kwallaye 2-0 a wasan na ranar Litinin, kuma Alexandre Lacazette ne ya taimakawa kungiyar ta Arsenal wajen jefa kwallayen baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.