Isa ga babban shafi
wasanni

Real Madrid ta samu nasarar farko a gidanta

A karon faroko cikin sabuwar kakar wasannin da muke ciki, kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasara a gida a fafatawar da ta yi da Espanyol a gasar La Liga ta Spain, in da suka tashi 2-0.

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo bai samu nasarar zura kwallo ba a wasan na jiya duk da hare-haren da ya kai a ragar Las Palmas
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo bai samu nasarar zura kwallo ba a wasan na jiya duk da hare-haren da ya kai a ragar Las Palmas Reuters / Paul Hanna Livepic
Talla

Dan wasan Real Madrid, wato Isco, shi ne ya zura kwallayen guda biyu a mintina na 30 da kuma 71.

Real Madrid mai rike da gambin gasar ta gaza samun nasara a wasanni guda 3 da ta yi a Santigao Bernabeu.

An dai yi ta daga tutar Spain a yayin fafatawar a Bernabeu, lura da cewa an yi wasan ne a ranar zaben raba gardama na ballewar Catalonia daga Spain.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.