Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta ci tarar kasashen Afrika

Kasashen Afrika na fuskantar fushin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA sakamakon saba dokokin hukumar a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni Infantino AFP
Talla

Amfani da dan wasan da bai dace ba da Gabon ta yi ya sa an ba Cote d’Ivoire nasara ci 3-0 akan Gabon.

Sannan an ci tarar Gabon kudi dala dubu shida da dari biyu.

FIFA ta ci tarar Najeriya kudi dala dubu talatin kan yadda ‘yan kallo suka fantsama a Uyo a wasan da Najeriya ta doke kamaru ci 4-0.

Jamhuriyar Congo za ta biya tarar kudi dala dubu 20 kan hargitsin da ya faru a lokacin da ta karbi bakuncin Tunisia a Kinshasa da suka tashi ci 2-2.

FIFa ta ci tarar Mali kudi dala dubu 15 saboda yadda ’yan kasar suka dinga fasa kwalabe da wurgo kujeru a fili a lokacin da ‘yan wasan kasar ke fafatawa da Morocco.

Sannan FIFA ta yi gargadi ga Senegal da Burkina Faso kan tsaikun soma wasa da suka yi a karawar da suka yi a Dakar da kuma Ouagadougou.

Tarar kudin dai babban kalubale ne ga kasashen na Afrika musamman diba da yadda hukumomin kwallon kasashen ke kai kawo wajen samun kudi daga gwamnatocin kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.