Isa ga babban shafi
wasanni

Ana shirin siyar da Newcastle ta Ingila

Wani kamfanin hada-hadar kudade karkashin jagorancin fitarciyyar ‘yar kasuwar Birtaniya Amanda Staveley ya kaddamar da shirinsa a hukumance na siye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle akan Pam miliyan 300

Rahotanni na cewa za a siyar da Newcastle akan farashin Euro miliyan 300
Rahotanni na cewa za a siyar da Newcastle akan farashin Euro miliyan 300 Reuters
Talla

Kamfanin na PCP Capital Partners ya shafe kimain wata guda ya na tattaunawa da mamallakin Newcastle Mike Ashley kan wannan batu.

Sai dai kawo yanzu, Newcastle ba ta sanar wa duniya halin da ake ciki ba duk da dai akwai wata majiya da ta musanta adadin kudin da aka ce za a siyar da kungiyar.

A ranar 16 ga watan Octoba ne Ashley ya bayyana cewa, yana son ya siyar da kungiyar bayan shekaru 10 da jagorantanta.

Kuma a shekara 2007 ne Ashley mai shekaru 53 ya karbi ragamar kungiyar, yayin da magoya bayanta ke yawaita yin zanga-znga kan yadda ya ke tafiyar da kungiyar.

Ashley ya siyi Newcastle ne akan Pam miliyan 134 a 2007, yayin da rahotanni ke cewa, a yanzu yana bukatar a ajiye ma sa Pam miliyan 380 kafin ya sallama ta ga wani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.