Seria A: An ci tarar kungiyar Verona euro dubu 20,000
Hukumar lura da gasar Seria A, ta ci tarar kungiyar Verona euro dubu 20,000, sakamakon yadda wasu magoya bayanta suka rika ihun furta kalaman nuna wariyar launi, ga dan wasan tsakiya na Juventus Matuidi.
Wallafawa ranar:
Magoya bayan na Verona sun fara muzanta Matuidi ne bayanda ya zura kwallo a ragarsu mintuna 6 da fara wasan, wanda a karshe Juventus din ta lallasasu da 3-1.
Haka ya sa a lokacin da yake yanke hukuci ka, Alkalin kotun sauraron kararrakin wasannin da ke Italiya Gererdo Mastrandrea, ya kara da cewa tilas kungiyar kwallon kafar ta Verona, ta buga wasa guda, ba tare da magoya bayanta sun shiga kallo ba, baya ga biyan tarar ta euro 20,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu