Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta kai matakin wasan karshe a gasar CHAN

Najeriya ta ta samu nasara kan Sudan da 1-0, a wasan matakin kusa da na karshe, na gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika na 'yan wasan dake fafatawa a kungiyoyi na gida, wato CHAN.

Wasu 'yan wasan Najeriya, yayin da suka samu nasarar doke kasar Sudan da 1-0 a gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika, ajin 'yan wasan da ke bugawa kungiyoyi na gida.
Wasu 'yan wasan Najeriya, yayin da suka samu nasarar doke kasar Sudan da 1-0 a gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika, ajin 'yan wasan da ke bugawa kungiyoyi na gida. completesportsnigeria
Talla

Hakan ke nufin Najeriya zata fafata wasan karshe na gasar ta CHAN a ranar Lahadi mai zuwa, da mai masaukin baki, wato kasar Morocco wadda ta lallasa kasar Libya da kwallaye 3-1 kafin kai wa matakin wasan na karshe.

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta fi kowace kasa lashe wannan gasa ta CHAN, wato ta cin kofin kwallon kasashen Afrika na 'yan wasan dake bugawa kungiyoyi na gida, domin ta dauki kofin wannan gasa sau 2, kuma yanzu haka ita ce mai rike da shi.

Jamhuriyar Congo ta dauki kofin na CHAN a shekarun 2009 da kuma 2016.

Kasar Tunisia ta zama zakara a shekarar 2011, yayinda Libya ta dauki kofin a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.