Isa ga babban shafi
Gasar cin kofin zakarun Turai

Ronaldo na ci gaba da haskawa a duniyar kwallon kafa

A fafata tsakanin Juventus da Real Madrid a matakin wasan dab da na kusan da karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a filin wasa na Allianz,dan wasa Christiano Ronaldo ya taka rawa  a nasarar da kungiyar sa ta samu a karawa da Juventus da ci 3 da nema. 

Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid
Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid Massimo Pinca/Reuters
Talla

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane wannan nasara na kara bashi damar  kare kanbin da kungiyar ke rike da shi a karo na uku a jere.

Juventus za ta yi kokarin rama abin da Real Madrid ta yi ma ta ranar 11 ga watan Afrilun nan.

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bukaci ‘yan wasansa da su maimata rawar da suka taka a filin Allianz.

Sevilla ta yi kasa  a guiwa a karawar ta da Bayern Munich da ta lashe kofin zakarun Turai sau biyar da ci 2 da 1.

Ronaldo mai shekaru 32 ya taimaka inda dan wasan ya zura kwallaye biyu a ragar Juventus,

Christiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu na Real Madrid a mituna 3 da mituna 64,bayan haka Marcelo ya zura kwallo na uku na Real Madrid a mituna 72 da wasa.

A yau Laraba Barca za ta karawa da  As Roma,sai wasa tsakanin Liverpool da Manchesterd City.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.