Isa ga babban shafi
wasanni

PSG ta karbe kofin Lig 1 daga hannun Monaco

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sake daukan kofin Lig 1 bayan ta yi ragaraga da Monaco mai rike da kambin da ci 7-1 a Parc des Princes.

Argentin Angel Di Maria ya taimaka wa PSG lashe kofin gasar Lig 1 a Faransa
Argentin Angel Di Maria ya taimaka wa PSG lashe kofin gasar Lig 1 a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Giovani lo Celso da Angel di Maria dukkaninsu sun zura kwallaye biyu-biyu, yayin da Edison Cavani da Julian Draxler suma suka jefa kwallo guda-guda.

Sai kuma Radamel Falcao na Monaco da ya ci gida.

A kakar bara ne dai, Monaco ta lashe kofin Lig 1 a karon farko cikin shekaru 17 , in da Falcao da Kylian Mbappe suka jagoranci kungiyar wajan lashe kofin a wancan lokaci, amma a bana ta gaza kare kanbinta.

Tuni dai Kylian Mbappe ya raba gari da Monaco, in da ya koma PSG akan farashin Pam miliyan 166.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.