Isa ga babban shafi
wasanni

Hukumar FIFA ta dauki mataki kan kalaman kyamar 'yan wasa a Rasha

Hukumar FIFA ta bayyana daukar matakin ladabtarwa ga wasu ‘yan kallo da suka yi wa wasu ‘yan wasa kalaman batanci na kiransu Birai a Rasha

Marseille doit impérativement marquer face à Leipzig.
Marseille doit impérativement marquer face à Leipzig. Odd ANDERSEN / AFP
Talla

Mai magana da yawun Hukumar FIFA ya ce Hukumar ta dauki matakin ladaftar da mai daukar bakuncin gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya wato kasar Rasha akan wasu kalamanatanci na kiran wasu ‘yan wasa dasunan Birai da aka ji wasu ‘yankallo na yi a lokacin da ake gudanar da wasar sada zumunci ta kasa da kasa tsakanin kasar da Faransa.

An ce dai masu kiran Biran na shagube ne gad an wasar tsakiya na Manchester United Paul Pogba da na Barcelona Ousmane Dembele ne a lokacin da aka ji su suna kiran Birai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP ya sanar.

To saidai ita kanta hukuymar kwallon kafa ta Rasha ta ce a shirye take ta bada hadin kai dangane da wannan batun na cin zarafi da aka ji wasu ‘yan kallo suna yi wa ‘yan wasar, har ma ita hukumar kwallon kafar ta Rasha na cewar sun kafa nasu kwamitin bincike akan wannan zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.