Isa ga babban shafi
wasanni

Ko Salah zai murmure kafin gasar kofin duniya?

Dan wasan Masar mai taka leda a Liverpool Mohamed Salah na da kwarin gwiwar murmurewa don halartar gasar cin kofin duniya duk da raunin da ya samu a kafadarsa a wasan karshe da suka fafata da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai a karshen mako.

Lokacin da Sergio Ramos ya yi Mohamed Salah keta a wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.
Lokacin da Sergio Ramos ya yi Mohamed Salah keta a wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai. REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Raunin ya tilasta wa Salah ficewa daga filin wasan cikin hawaye, lamarin da ya haifar da fargabar cewa, watakila  ya gaza samun damar wakiltan kasarsa a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Sergio Ramos na Real Madrid ne ya make hannun Salah a yayin fafutukar daukan kwallon, sannan ya kai shi kasa tare da dora masa nauyinsa, abin da wasu ke ganin cewa, da gangan Ramos din ya aikata haka.

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya bayyana raunin a matsayin mai girma kwarai kuma ana zaton kafadarsa ta goce.

Sai dai Salah mai shekaru 25 ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, yana da kwarin gwiwar haalartar  gasar cin kofin duniya a Rasha .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.