Ronaldo ya tsallake zaman gidan yarin shekaru biyu
Wata kotun birnin Madrid ta kasar Spain ta yanke wa gwarzon dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bayan ta same shi da laifin kauce wa biyan haraji.
Wallafawa ranar:
Koda yake kotun ta yi masa sasssauci, in da a yanzu ta dora masa biyan tarar Euro miliyan 18.8, tarar da tuni Ronaldo ya amice da ita.
Ronaldo ya isa harabar kotun ne a ranar Talata bayan kotun ta ki amincewa da bukatarsa ta farko ta bayyana a faifen bidiyo domin yi masa shari’a.
An zargi dan wasan ne da kin biyan haraji tsakanin shekarun 2010-2014, lokacin da yake kan ganiyar taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Ronaldo mai shekaru 33 na cikin attajiran ‘yan wasa a duniya, in da mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin na uku a jerin ‘yan wasan da suka fi arziki.
Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar a Turai, ya samu rakiyar budurwarsa, Georgina Rodriquez.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu