Isa ga babban shafi
wasanni

Schalke 04 na neman Moses na Najeriya

Kungiyar Kwallon kafa ta Schalke 04 da ke buga gasar Bundesliga ta Jamus, ta shiga cikin jerin manyan kungiyoyin Turai da ke neman kulla kwantiragi  da Victor Moses na Najeriya a daidai lokacin da ake ci gaba da cefanen 'yan wasa a wannan wata na Janairu.

Victor Moses
Victor Moses REUTERS/Darren Staples
Talla

Rahotanni na cewa, Schalke 04 na burin sayen Moses ne daga Chelsea domin taimaka ma ta a fafutukarta ta tsallake karewa a matakin ‘yan dagaji.

Akwai kungiyoyi irin su Fulham da Crystal Palace na Ingila har ma da Fernabache ta Turkiya da ke neman kulla kwantiragi da dan wasan.

Bisa dukkan alamu, Fernabache ta fi nuna cewa, a shirye take ta sauke kudaden saye da kuma biyan tsohon dan wasan na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.