Isa ga babban shafi
Wasanni

Sevilla ta lallasa Barcelona a gasar Cope del Rey

Sevilla ta samu nasarar doke Barcelona da 2-0, a zagayen farko na wasan da suka fafata a gasar cin kofin Cope Del Rey na kasar Spain.

Dan wasan gaba na kungiya Sevilla Wissam Ben Yedder yayin sadaukar da kwallo ta 2 da ya jefa a ragar Barcelona ga dan wasan Cardiff City  da ya bace a hadarin jirgi Emiliano Sala.
Dan wasan gaba na kungiya Sevilla Wissam Ben Yedder yayin sadaukar da kwallo ta 2 da ya jefa a ragar Barcelona ga dan wasan Cardiff City da ya bace a hadarin jirgi Emiliano Sala. Getty Images
Talla

‘Yan wasan kungiyar ta Sevilla Pablo Sarabia da Wissam Ben Yedder ne suka jefa mata kwallayen biyu a ragar Barcelona.

Bayan jefa kwallonsa Ben Yedder dan kasar Faransa, ya sadaukarta ita ga dan wasan Cardiff City Emiliano Sala, wadda har yanzu aka gaza gano shi, bayan hadarin jirginsu, da ya tashi daga Nantes zuwa South Wales.

Yayin wasan na Copa Del Rey zagayen kwata final, Barcelona ta hutar da gwarzon dan wasanta Lionel Messi, inda ta baiwa sabon dan wasanta Kevin-Prince Boateng damar buga wasan farko, ko da yake daga bisani Luis Suarez ya canje shi bayan hutun rabin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.