Isa ga babban shafi
Wasanni

Burin Juventus na zama gagara-badau ya gamu da cikas

Burin kungiyar Juventus na zama gagara-badau a gasar cin kofin Zakarun Turai ya gamu da cikas, bayan da a zagayen farko na matakin wasan kungiyoyi 16, Atletico Madrid ta lallasa su da 2-0 a ranar Laraba.

Dan wasan Atletico Madrid Jose Gimenez, yayin murnar jefa kwallo a ragar Juventus.
Dan wasan Atletico Madrid Jose Gimenez, yayin murnar jefa kwallo a ragar Juventus. REUTERS/Sergio Perez
Talla

‘Yan wasan Atletico Madrid Jose Gimenez da Diego Godin suka jefa kwallayen biyu a ragar Juventus, nasarar da ta baiwa kungiyar kwarin gwiwar fatan kaiwa zagayen wasannin kwata final.

Masu sharhi na ganin wasa zagaye na biyu da za’a fafata a Italiya ba zai yiwa Juventus sauki ba, ganin Atletico Madrid za ta yi bakin kokarinta wajen kaiwa wasan karshe na gasar ta zakarun Turai la’akari da cewa a filin wasanta za a fafata shi, ranar 1 ga watan Yuni da ke tafe.

A bangaren Juventus kuwa za ta yi fatan maimaita kokarin da ta nuna akan Real Madrid a kakar wasa ta bara, lokacin da ta rama kwallaye ukun da ta lallasata da su a zagayen farkon gasar zakarun Turan ta waccan lokacin, musamman ganin cewa tana tare da Cristiano Ronaldo a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.