Isa ga babban shafi
Wasanni

"Barcelona ce ta fi dacewa da Salah na Liverpool"

Tsohon dan wasan Chelsea, Samuel Eto’o ya bukaci Mohamed Salah na Masar da ya sauya sheka daga Liverpool ta Ingila zuwa Barcelona a Spain.

Mohamed Salah tare da hoton Lionel Messi na Barcelona
Mohamed Salah tare da hoton Lionel Messi na Barcelona REUTERS/Andrew Boyers & Sergio Perez/File Photo
Talla

Tun shekarar 2017 Salah ke taka rawar gani a Liverpool, inda ya ci mata kwallaye 54 a  cikin wasanni 74.

An dai yi ta rade-radin cewa, Salah zai koma Real Madrid amma, Eto’o na ganin cewa, Barcelona ce za ta fi dacewa da dan wasan na Liverpool.

Eto'o wanda ya yi shekaru biyar a Barcelona tun daga shekarar 2004, ya ce, Real Madrid ce silar tafiyarsa Turai daga Afrika, amma yana da masaniya kan tsarin Barcelona, don haka kungiyar ce tafi dacewa da Salah

Eto'o ya ce, Salah na da duk abinda ake bukata domin zama daya daga cikin zaratan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.