Isa ga babban shafi
Wasanni-Afrika

CAF ta sanya ranakun wasannin gasar cin kofin Afrika na 2021

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta bayyana watannin Janairu da Fabarairun shekarar 2021 a matsayin lokacin da za ta karbi bakoncin gasar cin kofin nahiyar da zai gudana badi, bayan tun farko ta janye daga daukar nauyin gasar ta bara da Masar ta karba.

Gasar cin kofin Afrika.
Gasar cin kofin Afrika. MOHAMED EL-SHAHED / AFP
Talla

Bayan ganawa da shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Ahmad Ahmad a Yaounde yayin ziyarar da ya kai Kamarun, sanarwar hadin gwiwa tsakanin hukumar kwallon kafar kasar da kwamitin shirya gasar ta cin kofin Afrika ta bayyana cewa gasar za ta gudana ne tsakanin ranakun 9 ga watan Janairun shekarar ta 2021 zuwa 6 ga watan Fabarairu.

Haka zalika sanarwar ta daban da CAF ta fitar, ta ce Kamaru da kanta ta bukaci sauya lokacin daga watan bakwai zuwa watan 1 dana biyu saboda gujewa gudanar da gasar a lokacin mamakon ruwa.

Gasar ta bara da Masar ta karbi bakoncin irinta ta farko da ta kunshi tawagar kasashe 24 wadda Algeria ta lashe, a wancan lokaci ma an sauya lokacin gasar ne saboda kaucewa gudanar da ita lokacin tsananin zafi a yankin arewacin Afrikan.

Acewar CAF sun yi kokari wajen ganin kwanakin wasannin gasar basu ci karo da lokacin da ake tsaka da wasannin gasar Turai ba, don baiwa ‘yan wasan Afrika da ke taka leda a Turai cikakkiyar damar takawa kasashensu leda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.