Isa ga babban shafi
Wasanni

Turai na adawa da shirin gudanar gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2

Gasar Firimiya Lig ta ingila ta shiga rukunin takwarorinta na sauran manyan kasashen Turai wajen adawa da shirin hukumar FIFA wajen maida gudanar gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru 2 a maimakon 4.

Tambarin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA.
Tambarin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA. AP - ENNIO LEANZA
Talla

Tun bayan fara gasar cin kofin duniyar a shekarar 1930 ne dai ake gudanar da ita duk bayan shekaru 4, amma banda tsakanin 1942 zuwa 1946 saboda yakin duniya na biyu.

Zalika gasar kwallon kafar ta cin kofin duniya ajin mata ma haka abin yake wajen gudanar ta duk bayan shekarun 4, tun bayan fara buga ta a shekarar 1991.

Yanzu haka dai tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger da a yanzu ke shugabantar sashin bunkasa kwallon kafa na hukumar FIFA, na ci gaba da fafutukar ganin ya gamsar da shugabannin hukumomin kwallon kafa a matakin nahiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki, kan su amince da gajarce lokacin shirya gasar kwallon kafar ta cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.