Messi ya nuna wa magoya bayan PSG kyautar Balon d'Or da ya lashe
Lionel Messi ya nuna wa magoya bayan PSG kyautar gwarzon dan kwallon duniya da ya lashe ranar Laraba, amma dan kasar Argentina din bai taka rawar gani ba a wasan da Nice ta rike PSG, mai jagorancin gasar Ligue 1 canjaras, babu ci har gida.
Wallafawa ranar:
Kafin wasan sai da aka bayyana shakkun ko Messi mai shekaru 34 zai fafata a wasan sakamakon ciwon ciki da ya yi fama da shi bayan da ya fita yawon walimar murnar lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya karo na 7 a ranar Litinin.
Sai dai duk da rade radin, ya fara wasan a cikin tawagar da babu Neymar, wanda ake ganin zai yi jinyar makonni 8 sakamakon rauni da ya ji a idon sawunsa, koma baya na baya bayan nan ga dan kasar Brazil din a birnin Paris.
Angel Di Maria da Kylian Mbappe sun kusan jefa kwallaye a raga bayan hutun rabin lokaci, amma abin ya ci tura. Su ma Nice ta hannun Kasper Dolberg sun kusan saka kwallo a raga, haka dai aka tashi wannan wasa babu ci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu