Isa ga babban shafi
'Yan bindiga

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi ya tsallake rijiya da baya

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi da ke Najeriya Kanar Sama‘ila Yombe Dabai ya tsallake rijiya da baya, lokacin da ‘yan bindiga suka kaddamar da hare hare a kauyen Kanya abinda yayi sanadiyar rasa rayuka da dama.

'Yan bindiga.
'Yan bindiga. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Rahotanni sun ce daga cikin mutane 19 da suka mutu a harin har da jami’an tsaron dake tawagar mataimakin Gwamnan da suka hada da sojoji da kuma ‘yan sanda.

Wannan kazamin harin na zuwa ne kwana guda bayan harin da aka kai Anene inda aka hallaka Yan Sakai sama da 60 a yankin.

Jihar Kebbi na ci gaba da fuskantar munanan hare haren ‘yan bindiga wadanda ke hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.