Isa ga babban shafi

Zinedine Zidane na bikin cika shekaru 50 da haihuwa

A yau alhamis ne tsohon tauraron kwallon kafar kasar Faransa Zinedine Zidane ke bikin cikon shekaru 50 da haihuwa. Zinedine Zidane ya gina rayuwar sa  ne a matsayin dan wasan kwallon kafa kamar wasu daga cikin taurarun yan wasan Faransa.

Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane.
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane. AP - Francisco Seco
Talla

Zinedine Zidane ya shiga tarihi ne  yayin wasa da ta hada kungiyar kwallon kafar Faransa da kungiyar kwallon kafar Tcheque,yayin wannan  fafatawa ne Zinedine Zidane ya zura kwallaye biyu a ragar kungiyar Tcheque.

Zinedine Zidane ya taka muhimiyar rawa a zamanin da yake taka tamola da kungiyar ta Faransa, ya taka leda a Real Madrid daga 2001 zuwa 2006 tarda lashe kyaututtuka da dama.

Ya kuma yi fama da fadi tashi kamar ko wane dan wasa,Zidane ya kasance mai bayar da shawara a kungiyar Real Madrid yan lokuta bayan dakatar da taka tamola a Real Madridf,kafin daga bisali ya zama mai horar da kungiyar a tsakiyar shekara ta 2016.

Tun shekara ta  2021, Zinedine Zidane ba shi da kungiya, duk da cewa ana ci gaba radin radin cewa akwai yiyuwar kasancewar sa da kungiyar PSG.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.