Isa ga babban shafi

PSG na shirin sanar da sunan kocin da zai maye gurbin Pochettino

Ana saran kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sanar da batun kulla yarjejeniya da Christophe Galtier matsayin mai horarwa don maye gurbin Mauricio Pochettino a yau talata yayin taron manema labaran da zakarar ta Faransa ta kira.

Mauricio Pochettino mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG.
Mauricio Pochettino mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG. AP - Manu Fernandez
Talla

Da misalin karfe biyu na ranar yau ne PSG za ta gudanar da gagarumin taron manema labaran a filin wasanta na Parc des Princes wanda wasu ke ganin kungiyar na son amfani da damar don gabatar da Galtier a matsayin sabon mai horarwa.

Duk da cewa kungiyar ta ki amsa tambayoyi game da gabatar da Galtier wasu faya-fayan bidiyo sun nuna dattijon mai shekaru 55 ya isa kungiyar a yammacin jiya litinin.

Tsawon makwanni 4 kenan ana dakon sanarwar PSG game da sabon mai horarwa yayinda Pochettino da tawagar mataimakansa ke ci gaba da aiki.

Wasu bayanai na cewa Galtier da ya shafe shekara guda yana horar da Nice na shirin kulla kwantiragin shekaru 2 da PSG dai dai lokacin da Pochettino ke shirin raba gari da kungiyar bayan shafe watanni 18 tare da dage kofin Lig 1 koda yak e shima kamar wadanda suka gabace shi ya gaza abin kirki a gasar cin kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.