Isa ga babban shafi

Bayern ta alwashin kawo karshen rashin tabbas kan makomar Lewondoski

Abinda tauraron Bayern Munich Robert Lewandowski ke gudu ya kusa samunsa, la’akari da cewar dole dan wasan ya bayyana a harabar kungiyar tasa a yau Laraba, domin shiga sansanin atasayenta na tunkarar sabuwar kakar wasa, duk kuwa da cewar ya dade yana nanata aniyarsa ta son rabuwa da zakarun na gasar Bundesliga.

Tauraron kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski.
Tauraron kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski. AP - Matthias Schrader
Talla

Wata majiya ta ruwaito cewar Lewondoski na da kwarin gwiwar cewar nan ba da jimawa ba za a cimma yarjejeniya tsakanin Barcelona da Bayern Munich kan sauyin shekarsa zuwa Spain.

Bayern dai na son cigaba da rike dan wasan na ta, sai dai babu damar tilasta masa, abinda ya sanya ta tasayar da farashin Yuro miliyan 50 ga duk kungiyar dake neman kulla yarjejeniya da shi.

Wasu masu sharhi dai na ganin lamarin zai yi wa Barcelona wahala, la’akari da cewar burinta shi ne kashe kasa da adadin kudin da Bayern ta ware domin sayen Lewondoski, zalika babu alamun zakarun na Bundesliga za su sassauto.

A halin da ake ciki yanzu, shugabanin Bayern sun cimma matsayar nemo mafita kan makomar tauraron nasu kafin ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.