Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta kammala kulla yarjejeniya da Mane

Kungiyar Bayern Munich ta tabbatar da kammala kulla yarjejeniya da Sadio Mane a yau Laraba daga kungiyar Liverpool, inda tace dan wasan daga kasar Senagal ya rattaba hannu akan kwantiragin da zai shafe shekaru 3 tare da zakarun na gasar Bundesliga.

Sadio Mane bayan kulla yarjejeniya da kungiyar Bayern Munich.
Sadio Mane bayan kulla yarjejeniya da kungiyar Bayern Munich. © AP - Sven Hoppe
Talla

Bayanai sun ce Bayern ta biya Liverpool euro miliyan 41 kafin kammala kulla yarjejeniya da dan wasan.

A tsawon shekaru 6 da ya shafe tare da ita, Mane mai shekaru 30 ya taimakawa Liverpool lashe kofunan da suka hada da na gasar Zakarun Turai 1, gasar Firimiyar Ingila, kofin FA, da na Carabao, da kuma na  Club World Cup.

Mane ya ci wa Liverpool kwallaye fiye da 100 cikin shekaru 6

Baya ga kofuna, Mane ya ci wa Liverpool jumillar kwallaye 120 cikin wasanni 269 da ya buga.

Tun da farko Mane ya rabu da kasarsa Senegal yana da shekaru 19, inda ya fara buga kwallon kafar matakin kwararru a kungiyar Metz dake Faransa, inda ya shafe shekara guda, kafin ya kuma koma kungiyar RB Salzburg. dake Jamus.

A shekarar 2014 ya koma gasar Firimiyar Ingila bayan kulla yarjejeniya da Southampton, a 2016 kuma ya koma Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.