PSG ta kulla yarjejeniya da Fabian Ruiz na Spain daga Napoli
Dan wasan tsakiya na kasar Spain, Fabian Ruiz ya koma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain da taka leda daga Napoli kan yarjejeniyar shekaru biyar.
Wallafawa ranar:
Dan wasan dai shi ne na biyar da PSG ta kulla yarjejeniya da shi a baya bayan nan domin karfafa bangaren tsakiyarta bayan zuwan ‘yan wasan Portugal biyu wato Vitinha da Renato Sanches dukkaninsu a cikin wannan kaka.
Fabian mai shekaru 26 ya shafe shekaru hudu tare da Napoli, inda ya yi nasarar lashe mata kofin Italia a shekarar 2020.
Akwai dai kyakkyawan fatan Fabian ya taimakawa tsakiyar PSG musamman dai dai lokacin da kungiyar ke fatan ganin ta yi rawar gani a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai na kakar da muke ciki, bayan rikitowarta a wasannin gab da na karshe na kakar da ta wuce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu