Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta kawo karshen fatan PSG na lashe kofin zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kawo karshen fatan PSG na lashe kofin zakarun Turai cikin wannan kaka, bayan da ta lallasata da kwallaye biyu da nema a wasansu na daren jiya laraba. 

Wasan jiya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta PSG da Bayern Munich karkashin gasar zakarun Turai.
Wasan jiya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta PSG da Bayern Munich karkashin gasar zakarun Turai. REUTERS - KAI PFAFFENBACH
Talla

Tun a haduwar farko dama Bayern Munich ta lallasa PSG da kwallo 1 mai ban haushi har gidanta cikin watan jiya, gabanin nasarar ta daren jiya wanda ke nuna tauraruwar ta Jamus ta doke zakarar ta Faransa da kwallaye 3 da nema a jumlace.

Cikin shekaru 11 da PSG ta shafe ta na fafutukar ganin ta lashe kofin na zakarun Turai, wannan ne karo na biyu a jere da ake cire kungiyar a matakin zagaye na biyu a gasar kuma karo 5 a cikin shekaru 7. 

‘Yan wasan kungiyar Kylian Mbappe da Lionel Messi basu taka rawar ganin da aka saran za su taka yayin wasan na jiya ba lamarin da ya ja musu kakkausar suka musamman Messi wanda kungiyar ta zuba makudan kudi wajen sayenshi don ganin ya kawo mata kofin na zakarun Turai.

Sai dai anga yadda Sergio Ramos yayi kokarin dawo da PSG a wasan na jiya yayin wasu hare-hare biyu da ya kai amma yunkurin na sa ya ci tura. 

Tsohon dan wasan Ingila Owen Hargreaves da ke sharhi kan wasan na jiya, ya ce abin kunya ne yadda PSG ta tattara tarin matasa kuma zakakuran ‘yan wasa masu matukar tsada amma a ko da yaushe take ci baya maimakon gaba.

Manajan PSG Christope Galtier y ace abin takaici ne yadda suka rasa damar kaiwa gaba a gasar ta zakarun Turai amma dole su karbi gaskiyar cewa sun tamkar kuskure tare da laluben hanyar gyara.

Tun bayanda ‘yan kasuwar Qatar suka karfi ragamar kungiyar ta PSG a shekarar 2012 ta kasha kudin da ya haura dala biliyan 1 wajen sauya fasalin kungiyar tare da mayar da ita gagarabadau tsakanin takwarorinta inda zuwa yanzu ta lashe kofunan Lig 1 guda 8 sai kofunan kananun gasar cikin 12.

Amma har zuwa yanzu kungiyar ta gaza lashe kofin na zakarun Turai, inda suka yi rashin nasara a wasan karshe na cin kofin gasar a shekarar 2020 a hannun Bayern Munich.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.