Isa ga babban shafi

PSG ta sake shan kaye har gida da kwallaye 2 da nema a hannun Lyon

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sake shan kaye karo na 2 a gidanta hannun Lyon da kwallo 1 mai ban haushi, rashin nasarar da ya rage tazarar makin da jagorar ta Ligue 1 ke da shi zuwa maki 6 tsakaninta da Lens mai biye da ita.

Wasan PSG da Lyon a jiya lahadi
Wasan PSG da Lyon a jiya lahadi REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Wasan na jiya da ke zuwa makwannni 2 bayan rashin nasarar PSG a gida hannun Rennes da kwallaye 2 da nema, dan wasan Lyon Bradley Barcola ne ya zura kwallon daya tilo da ta bai wa tawagar ta Galtier ciwon kai a filin wasa na Parc de Princes.

Bradley Barcola dai ya shiga fili ne a matsayin sauyi ga Aminu Sarr da ya samu rauni, mintuna kalilan bayan rashin nasarar Alexander Lacazette a bugun fenariti.

Rashin nasarar ta jiya dai na matsayin karo na 5 da PSG ke shan kaye cikin wannan kaka karkashin jagorancin Christophe Galtier.

A bangare guda Lyon wadda tsohon manajan PSG Laurent Blanc ke jagorancinta, nasarar ta bata damar komwa ta 9 a teburin Lig 1 da maki 44 tazarar maki 22 tsakaninta da PSG da ke jagoranci teburi da maki 66.

Dan wasan tsakiyar PSG Danilo a zantawarsa bayan rashin nasarar ya ce wajibi ne a gare su, su farka lura da yadda suke kara bayar da dama ga Lens da ke biye da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.