Isa ga babban shafi

Mane zai biya tara mafi tsauri a tarihin Bayern Munich

Bayern Munich ta lafta wa dan wasanta na gaba Sadio Mane tarar fam 260,000, sakamakon naushin da ya kirba  wa abokin wasansa Leroy Sane a makon da ya gabata.

Sadio Mane
Sadio Mane AP - Jon Super
Talla

An dai bai wa hammata iska tsakanin ‘yan wasan biyu ne a dakin sauya kaya, jim kadan bayan da Manchester City ta lallasa Bayern Munich da kwallaye 3-0 a wasan farko na zagayen kwata final a gasar zakarun Turai, ranar Talatar da ta gabata.

Babu da Karin haske akan dalilin da ya janyo fadan da aka Mane da sane suka yi, wanda tun a cikin filin wasa suka fara cacar baka.

Wasu rahotanni dai sun ce baya ga haramta mishi buga wasa guda, da kuma tarar da aka yanka masa, a halin yanzu kungiyar ta Bayern na duba yiwuwar sayar da Mane a karshen kakar wasa ta bana.

Tarar da Bayern Munich ta lafta wa Sadio Mane dai, ita ce mafi girma da ta taba yanka wa wani dan wasa a tarihin kafuwarta.

A baya bayan nan, kocin Bayern Munich Thomas Tuchel y aba da tabbbacin cewa, Mane zai haska a wasa na biyu a zagayen kwata final din gasar zakarun Turai da za su kara da Manchester City a ranar Laraba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.