Isa ga babban shafi

Chelsea na bukatar bullo da sabon salo - Silva

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thiago Silva, ya ce kungiyar na bukatar bullo da wasu sabbin dabaru, ko kuma ta sake fuskantar koma baya mafi muni a kakar wasa mai zuwa.

Dan wasan Chelsea, Thiago Silva kenan.
Dan wasan Chelsea, Thiago Silva kenan. AFP/File
Talla

Duk da makudan kudade da aka kashe a hannun sabon mai kungiyar Todd Boehly, Chelsea tana mataki na 11 a gasar Premier kuma za ta kare a kakar bana ba tare da kofi ba bayan da Real Madrid ta doke ta a gasar zakarun Turai.

Hukumomin Chelsea, sun kashe sama da Yuro miliyan 550 a wannan kaka, da kuma hada-hadar ‘yan wasa, domin inganta tawagar ‘yan wasa 30, amma hakan babu abin da ya haifar mata, face rashin nasara.

Chelsea ta kori kocinta Thomas Tuchel da Graham Potter a kakar wasa ta bana, yayin da kocin rikon kwarya Frank Lampard ya yi rashin nasara a dukkanin wasanni hudun da ya yi tun lokacin da ya karbi ragamar horar da kungiyar a karo na biyu a wannan watan.

Rahotanni sun bayyana cewa Chelsea ta tattauna da tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann a wani bangare na neman sabon koci, kuma daga cikin wandanda kungiyar ke ruwan ido a kan su akwai tsohon kocin Spain Luis Enrique.

Tsohon dan wasan kungiyar ta Chelsea, Didier Drogba, ya ce bai san inda kungiyar ta nufa ba a halin yanzu idan aka kwatanta da lokacin da ya buga wasa a Stamford Bridge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.