Isa ga babban shafi

Kyautar Marc-Vivien Foé: Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare

Dan wasan tsakiya na Ivory Coast Seko Fofana, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon Afirka a gasar Ligue 1 a shekarar 2022, yana cikin jerin 'yan wasa 11 da aka zaba a shekarar 2023 na gwarzon Marc-Vivien Foé.

'Yan takara 11 (daga hagu zuwa daman karshe) Achraf Hakimi, Chancel Mbemba, Habib Diallo, Hamari Traoré, Mama Baldé, Marshall Munetsi, Mohamed Camara, Salis-Abdul Samed, Séko Fofana, Terem Moffi, Yunis Abdelhamid
'Yan takara 11 (daga hagu zuwa daman karshe) Achraf Hakimi, Chancel Mbemba, Habib Diallo, Hamari Traoré, Mama Baldé, Marshall Munetsi, Mohamed Camara, Salis-Abdul Samed, Séko Fofana, Terem Moffi, Yunis Abdelhamid © Photos AFP-Reuters/montage RFI
Talla

RFI da France 24 za su bayyana wanda ya yi nasara a ranar 30 ga watan Mayu.

ABDELHAMID Yunis

Dan wasan bayan Morocco da Reims, wanda aka zaba a bara, ya zo matsayi na uku a shekarar 2020, dan wasan mai shekaru 35 ya haskaka a lokacin gagarumin ci gaban da kungiyar ta samu, inda ta yi wasanni 19 a jere ba tare da tayi rashin nasara ba.

BALDÉ Mama

Ya kasance dan wasan gabana kasar Guinea-Bissau da kuma kungiyar Troyes.Baldé ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin ’yan wasan da suka taka rawar gani a Troyes, duk da fadawar da kungiyar ta yi a rukunin ‘yan dagaji na gasar Ligue 1.          

CAMARA Mohamed

Dan wasan tsakiya na kasar Mali, da kuma a Monaco ta kasar Faransa, mai shekaru 23, wanda aka dauka a matsayin wanda zai maye gurbin Aurélien Tchouaméni, wanda ya koma Real Madrid, , ya kasance mai karsashi da fafutuka ga kungiyar da ke neman zuwa gasar zakarun Turai.

DIALLO Habib

Ya kasance dan wasan gaba ga tawagar kwallon kafa ta kasar Senegal da kuma Strasbourg.

Duk da gwagwarmayar Strasbourg, dan wasan mai shekaru 27 ya kasance daya daga cikin wadanda suka taka rawa, wajen cimma burinsu. Gudun mowar da Diallo ya bayar ga kungiyar a wannan kaka, ya taimaka mata wajen kasancewa cikin kungiyoyin da suke kan gaba-gaba a saman teburi.

FOFANA Seko

Ya kasance dan wasan tsakiya na kasar Côte d’Ivoire da kuma Lens.

Ana masa lakabi da gwarzo a tsakiya filin wasa , Fofana ya damar lashe kyautar wannan gasa ta shekarar 2022. Matashin mai shekaru 27 kungiyarsa na fafutukar yadda za ta kubucewa kalubalen da suka dabaibaye ta.

Ko da yake, ana sa ran Fofana zai kasance a cikin fafutukar neman kungiyarsa ta samu gurbi cikin wuraren da suka rage a saman teburin Ligue 1 domin samun gurbi a gasar zakarun Turai da za a yi a kakar wasa mai zuwa.

HAKIMI Achraf

Fitaccen dan wasan bayan Morocco da kuma PSG

Dan wasan da ake yiwa ikirari da mai hazaka, kuma mai taka tsan-tsan wajen kai hari. Ya kasance daga cikin tawagar da suka taimaka wa Morocco kafa tarihi a gasar ccin kofin duniya ta 2022 da aka yi a kasar Qatar.

Hakimi ya kawata tarihinsa bisa irin gudun mowar da ya bawa PSG ci gaba da kasancewa a sahun gaba a gasar ta Ligue 1.

MBEMBA Chancel

Dan wasan bayan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma Marseille, ya kasance dan wasan baya mai naci, mai shekaru 28 ya bayar da mamaki kwarai wajen taimakawa kungiyar samun nasarori a wannan kaka.

MOFFI Terem

Ya kasance dan wasan gaba a tawagar kwallon kafa ta Najeriya da kuma Nice.

Daya daga cikin ‘yan wasan gaba da ke kai wa abokan hamayya hari a filin wasa, Teremas Igobor Moffi ya yi kaura daga Lorient zuwa Riviera a cikin Janairun 2023. Dan wasan mai shekaru 23 ana alakanta shi da mai basira da kuma jajircewa.

MUNETSI Marshall

Yana daga cikin ‘yan wasan tsakiya na kasar Zimbabwe da kuma kungiyar kwallon kafa ta Reims da ke fafatawa a gasar Ligue 1.

Muneti ya samu ci gaba a karkashin Will Still la’akari da irin gudun mowar da yake takawa wajen kai hari.

TRAORÉ Hamari.

Dan wasan baya ga tawagar kwallon kafa ta kasar Mali da kuma Rennes da ya kasance mai zafin nama da kuma naci.

Mai tsaron ragar Rennes ya fito a cikin jerin ‘yan wasan da sunansu ya fito a wannan gasa ta Marc Vivien Foé, la’akari da irin namijinn kokarin da ya yiwa tawagar Rennes a Turai.

SAMED Salis Abdul

Dan wasan tsakiya na kasar Ghana da kuma kungiyar kwallon kafa ta Lens.

An dauke shi aiki a farkon kakar wasa bayan shekaru biyu a Clermont-Ferrand, kuma dan wasan mai shekaru 23, ya buga dukkan wasannin Ghana uku a gasar cin kofin duniya ta 2022 kuma inda ake ganin zai bayar da mamaki ga tawagar Lens, musamman wajen bata gudun mowa a daya daga cikin wasannin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.