Isa ga babban shafi

PSG za ta hukunta Messi kan tafiya Saudiyya ba tare da izinin ta ba

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kafa kwamitin ladaftarwa don gudanar da bincike kan dan wasan gabatan ta Lionel Messi, wanda ka iya fuskantar dakatarwa saboda tattakin da yayi zuwa Saudi ba tare izinin kungiyar ba. 

Lionel Messi wa PSG
Lionel Messi wa PSG AP - Aurelien Morissard
Talla

Kafofin yada labarai da dama sun ruwaito cewar zakaran gasar cin kofin duniya ka iya fuskantar dakatarwa na tsawon makwanni biyu, amma sai dai majiyar kungiyar da kamfanin dillancin labarai na Faransa ta zanta da ita, ta ce dakatarwar ba zata wuce ta kwanaki ba. 

Dan wasan da zai cika shekaru 36 a watan gobe, ya buga wasan da kungiyar sa ta sha kashi a gida a hannun Lorient a gasar Ligue 1 ranar Lahadi. 

Sai dai bayan haka, Messi ya yi tattaki zuwa Saudiya don gudanar da harkokin kasuwanci, duk da ya ke mai horas da su ya dakatar da hutun da ya kamata su samu.  

A shekarar 2021 ne dai, Messi da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau 7 ya bar kungiyar Barcelona inda ya koma PSG, kuma ya samu nasarar zurawa kungiyar kwallaye 31 daga cikin wasanni 69 da ya buga mata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.