Al Ahly ta lashe kofin zakarun nahiyar Afrika karo na 11
Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly a Masar ta lashe kofin zakarun nahiyar Afrika karo na 11 bayan doke Wydad Casablanca ta Morocco a birnin Cairo.
Wallafawa ranar:
Kwallon mai tsaron baya na Al Ahly Mohamed Abdelmonem ce ta taimakawa kungiyar samun kofin bayan da ta basu damar yin canjaras da kwallo 1 da 1 a haduwar ta jiya.
Tun farco Wydad ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Yahia Attiyat amma kuma farkewar Abdelmonem ya baiwa Al Ahly nasara fa fifikon kwallayenta 2 na haduwarsu ta farko, inda a jumulla suka tashi wasa 3 da 2.
Cikin wannan kaka Ahly ta zura kwallaye 27 ciki har da 4 da Abdelmonem ya zura wanda suka bata damar kwace kambun na zakarun nahiyar Afrika daga hannun Wydad da ta lashe a bara.
Nasarar ta Al Ahly ta kawo karshen shan kayen da kungiyar ta yi har sau 2 a wasannin karshe hannun Wydad.
Sabanin Turai, karkashin gasar ta Afrika har yanzu kwallo a waje na da maki biyu ne yayinda ta gida ke da maki guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu