Isa ga babban shafi

United ta amince da sallamin sama da Fam miliyan 47 don dauko Andre Onana

Manchester United ta amince da sallamin Fam miliyan 47 da dubu dari 2 kwatankwacin Yuro miliyan 55, don dauko mai tsaron ragar Inter Milan Andre Onana.

Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana da Manchester United ke kokarin dauko wa daga Inter Milan.
Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana da Manchester United ke kokarin dauko wa daga Inter Milan. REUTERS/Massimo Pinca
Talla

United na fatan kammala cinikin dan wasan har ma ta yi tattaki da shi zuwa Amurka, a wasannin sada zumunci don shiryawa kakar da za’a fara a watan gobe.

Onana dan asalin Kamaru mai shekaru 27 da zai maye gurbin David De Gea da ya rabu da kungiyar a makon jiya bayan shafe shekaru 12, zai sanya hannu ne a kwantaragin shekaru 5 da zabin karin shekara daya.

Mai horas da kungiyar Erik ten Hag ya nuna sha’awar kawo mai tsaron ragar wanda ya taba horaswa a lokacin da ya ke kungiyar Ajex.

Idan har wannan ciniki ya tabbata, Onana zai zama dan wasa na biyu da United ta saya cikin wannan kaka bayan Mason Mount daga Chelsea kan Yuro miliyan 55.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.