Isa ga babban shafi

Super Falcons na shirin doka wasanta na farko da Canada mai rike da kambu

A gobe Juma’a ne, tawagar Super Falcons ta Najeriya za ta buga wasanta na farko a gasar lashe kofin duniya ta mata a rukunin B da Canada, wacce ke rike da kofin gasar Olympic ta mata. 

Tawagar kungiyar kwallon kafar Mata ta Najeriya Super Falcons.
Tawagar kungiyar kwallon kafar Mata ta Najeriya Super Falcons. Pulse.ng
Talla

Sau tara tawagar ta Najeriya na halartar gasar, inda a shekarar 1999 ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa tarihin kai wa matakin daf da na kusa da na karshe, wanda babu wata kasa daga nahiyar Afrika da ta taba kai wa matakin.  

A gasar ta karshe da kasar da ke yammaci Afrika ta halarta, Faransa ce ta fitar da ita a matakin zagaye na biyu na gasar. 

A yanzu tawagar ta Super Falcons na kokarin kafa sabon tarihi, bayan nasarar lashe wasanni 4 kacal daga cikin 26 da ta taba dokawa karkashin wannan gasa ta lashe kofin duniya ta mata. 

Nahiyar Afrika dai ta samu wakilcin kasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da Morocco da kuma Zambia a gasar ta bana da aka fara a yau. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.