Isa ga babban shafi

United za ta fayyace makomar Greenwood kafin fara sabuwar kakar wasa

Manchester United za ta yanke hukunci kan makomar dan wasanta Mason Greenwood kafin fara kakar wasa ta bana, inda a wasan farko za ta kara da kungiyar Wolves a ranar 14 ga Agusta.

Dan wasan Manchester United Mason Greenwood
Dan wasan Manchester United Mason Greenwood POOL/AFP
Talla

A farkon watan Fabarairun da ya gabata ne kotu ta soke tuhume-tuhumen da Greenwood mai shekaru 21 ke fuskanta akan yunkurin aikata fyade da kuma cin zarafin wata budurwa.

Sai dai bayan janye shari’ar, Manchester United ta sanar da kaddamar da na ta binciken kan zargin da aka yi wa dan wasan na ta.

Greenwood wanda yarjejeniyarsa da United za ta kare a watan Yunin shekarar 2025, bai koma atasaye da kungiyar ta  sa ba, ballantana buga mata ko da wasa guda tun bayan tuhume-tuhumen da ya fuskanta  zuwa bayan janye su da aka yi.

A ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2019 Mason Greenwood ya fara buga wa Manchester United wasa yayin karawarta ta Arsenal, a lokacin da yake da s hekaru 17.

Wasanni 83 ya buga wa United a gasar Frimiya, inda ya ci kwallaye 22, ya kuma taimaka aka jefa wasu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.