Isa ga babban shafi

PSG: Da yuwuwar Kylian Mbappe ya sanya hannu kan sabon kwantiragi

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe ya dawo atisaye a kungiyar kuma da alama zai ci gaba da zama a kungiyar a wannan kakar.

PSG ta ce an maido da Mbappe ne bayan doguwar tattaunawa da aka yi.
PSG ta ce an maido da Mbappe ne bayan doguwar tattaunawa da aka yi. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

Dan wasan gaban Faransa, mai shekara 24, bai yi atisaye da ‘yan wasan ba, haka kuma baya cikin tawagar da ta PSG ta fafata da Lorient ranar Asabar, wanda suka tashi 0-0.

Dan wasan dai ya shiga tsaka mai wuya game da mafarkinsa na zuwa Real Madrid amma yanzu yana iya tsawaita kwantiraginsa a PSG.

PSG ta ce an maido da Mbappe ne bayan doguwar tattaunawa da aka yi.

Kyaftin din na Faransa ya kalli wasan da aka yi na ranar Asabar tare da Ousmane Dembele, wanda ya koma PSG daga Barcelona kan sama da yuro miliyan 45.

Ousmane Dembele daga dama, Kylian Mbappe daga tsakiya da kuma kaninsa Ethan Mbappe daga hagu, yayin kallon wasan da PSG ta kara da Lorient a ranar Asabar.
Ousmane Dembele daga dama, Kylian Mbappe daga tsakiya da kuma kaninsa Ethan Mbappe daga hagu, yayin kallon wasan da PSG ta kara da Lorient a ranar Asabar. © Prothom

Mbappe na da sauran shekara guda a kwantiraginsa na yanzu kuma kawo yanzu ya ki sanya hannu kan sabon kwantiragi.

A watan da ya gabata, PSG ta bai wa kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya izinin tattaunawa da dan wasan bayan ta kai tayin kusan yuro miliyan 300.

Shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi ya dage cewa ba zai bar dan wasan ya tafi a banza ba, inda ake ganin akwai yiwuwar Mbappe ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiragin na shekara guda.

Hakan zai kai 2025 kuma zai baiwa PSG damar sayar da Mbappe ga Real a kaka mai zuwa.

Mbappe, wanda ya koma PSG a shekarar 2017 da farko a matsayin aro daga Monaco kafin cinikin Euro miliyan 180, ya zura kwallaye 212 a wasanni 260 a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.