Isa ga babban shafi

Guardiola ba zai jagoranci wasa biyu da Man City za ta buga ba

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ba zai jagoranci wasanni biyu na Premier da kungiyarsa za ta buga ba sakamakon jinyar tiyatar baya da aka yi masa a birnin Barcelona.

Pep Guardiola a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wanda kungiyar Manchester City ta fafata da Inter Milan a filin wasa na Atatur da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya, ranar 10 ga watan Yuni, 2023.
Pep Guardiola a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wanda kungiyar Manchester City ta fafata da Inter Milan a filin wasa na Atatur da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya, ranar 10 ga watan Yuni, 2023. REUTERS - MURAD SEZER
Talla

Sanarwar da masu rike da kofin gasar Premier ta fitar, ta ce kocin nasu ya dade yana fama da ciwon baya kuma an yi masa tiyatar gaggawa a Barcelona.

Aikin tiyatar da aka yiwa Guardiola na samu nasara amma zai ci gaba da zaman jinya a birnin. Ba a sa ran kocin mai shekaru 52 ba zai dawo City ba har sai bayan hutun wasanni na kasa da kasa, wanda hakan ke nufin ba zai buga wasan da za su yi da Sheffield United a ranar Lahadin nan ba, da kuma tattaki zuwa gidan Fulham a ranar 2 ga Satumba.

Juanma Lillo wanda ya koma kungiyar a matsayin mataimakin koci a farkon wannan watan bayan ya yi jinya a matsayin kocin Al Sadd a Qatar zai dauki nauyin horo da wasanni na masu rike da kofin gasar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Man City ke wasanni ba tare da kocinta ba tun lokacin da Guardiola ya fara zuwa filin wasa na Etihad a shekarar 2016.

Haramcin buga gasar zakarun Turai a tsakiyar 2018 ya sanya Guardiola ya bawa Mikel Arteta damar ya jagoranci tattakin da kungiyar ta yi zuwa gidan Lyon a watan Satumba, a wasan rukuni-rukuni wanda City ta sha kashi da ci 2-1.

Sannan, a farkon shekarar 2022, Guardiola bai buga wasan zagaye na uku na gasar cin kofin FA a Swindon Town ba saboda fama da cutar Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.