Isa ga babban shafi

Hamayya ta kawo karshe a tsakanina da Messi - Ronaldo

Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa tabbas shi da takwaransa na Argentina Lionel Messi sun sauya tarihin kwallon kafa amma a yanzu dabin da suka shafe tsawon shekaru su na yi ya kawo karshe.

Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiyya a yanzu haka.
Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiyya a yanzu haka. © AFP - FAYEZ NURELDINE
Talla

‘Yan wasan biyu mafiya haskawa tare da nuna bajinta karkashin gasar La Liga a Spain sun shafe shekaru 15 suna wannan dabi inda Ronaldo ke matsayin tauraron Real Madrid a bangare guda Messi ke matsayin zakaran Barcelona, kungiyoyi biyu da ke da tarihin dabi a tsakaninsu.

Ronaldo mai shekaru 38 wanda yanzu hake ya ke taka leda da Al Nassr mai doka gasar lig din Saudiya ya ce duk da cewa su ba abokanai ne na kusa da Messi ba, amma su na matukar girmama junansu.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo yayin da suke fafatawa a gasar  La Liga.
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo yayin da suke fafatawa a gasar La Liga. AFP/Josep Lago

Ronaldo wanda ya lashe Ballon d’Or har sau 5 a tarihi, kalaman na sa, na zuwa ne a dai dai lokacin da karon farko cikin shekaru 20 aka fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da za su fafata wajen neman lashe kyautar gwarzon shekarar ta Ballon d’Or ba tare da anga sunan shi a jerin ba.

A cewar Ronaldo kowannensu ya zabi hanyar da ya ke ganin za ta bulle mishi amma kowannensu na ci gaba da dorawa ne akan manufofinsa.

Ronaldo da Messi su ne 'yan wasa mafiya lashe wannan kyauta ta Ballon d'Or a tarihi.
Ronaldo da Messi su ne 'yan wasa mafiya lashe wannan kyauta ta Ballon d'Or a tarihi. © AFP

Da ake tambayar shi ko dabin da ke tsakaninsu ya samo asali ne daga kiyayya Ronaldo ya ce bai kamata masu son shi a fagen kwallo su nuna kiyayya ga Messi ba, ya na mai cewa sam baya yi wa dabi tsakaninshi da Messi kallon kiyayya face kokarin nuna gogewarsu a fagen na tamaula cikin shekaru 15 da suka shafe suna kwallo a Turai.

 

Gwagwarmayar Messi da Ronaldo a La Liga

Ronaldo dai shi ke matsayin mafi zurawa Real Madrid kwallo da jumullar  kwallaye 451 a wasanni 438 inda ya lashe kofuna 16 ciki har da na zakarun Turai 4 da La Liga 2 sai Copa del Rey 2 a shekaru 9 da ya shafe a kungiyar ta Spain.

A bangare guda Messi mai shekaru 36 wanda yanzu ke taka leda da Inter Miami ta Amurka na matsayin mafi zurawa Barcelona kwallo a tarihi da kwallaye 674 a wasanni 781 tare da lashe kofuna 35 ciki har da La Liga 10 da kofin zakarun Turai 4 baya ga Copa del Rey 7.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo yayin wasan sada zumunta sakanin PSG da wasu kungiyar Saudiya a Riyadh 19/01/23.
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo yayin wasan sada zumunta sakanin PSG da wasu kungiyar Saudiya a Riyadh 19/01/23. © FRANCK FIFE / AFP

'Yan wasan biyu Ronaldo da Messi  da ake sanyawa a sahun gwarazan da suka fi yin fice a tarihin kwallo, sun hadu da juna sau 36 kuma haduwarsu ta karshe ita ce cikin watan Janairun shekarar nan inda PSG ta doke tawagar Saudiya da kwallaye 5 da 4 a Riyadh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.