Isa ga babban shafi

Jadawalin gasar cin kofin Afrika zai raba Najeriya, Morcco da Afrika ta kudu a rukuni

Hukumar kwallon kafar Afrika na shirin ware kasashen Najeriya da Afrika ta kudu da kuma Morocco a waje guda yayin rarraba kasashe a rukunnan tunkarar gasar cin kofin Afrika da ke tafe a badi, wanda ke nuna yiwuwar cewa kasashen 3 bazasu hadu da juna a matakin rukuni ba.

Senegal ke rike da kambun gasar wadda ke gudana duk bayan shekara biyu.
Senegal ke rike da kambun gasar wadda ke gudana duk bayan shekara biyu. © CAF Media Channel
Talla

Morocco wadda ke matsayin jagora a zubin kasashe 6 mafiya kwazo a Afrika, ta samu kaiwa matakin ne bayan nasararta ta kaiwa wasan gab da na karshe a gasar cin kofin duniya da ta gudana a Qatar bara, kuma za ta kasance a rukunin farko na jadawalin gasar yayinda Najeriya za ta zama a rukuni na biyu sai kuma Afrika ta kudu a rukuni na 3.

Hasashen jadawalin gasar ta cin kofin Afrika da zai gudana a birnin Abidjan na Ivory Coast ya nuna yiwuwar Gambia ta tsinci kanta a rukuni na 4, kasar da ta kai wasan gab da na karshe na makamanciyar gasar a 2021, kuma ana ganin bangaren rukunin nata ya kasance mafi hadari.

Super Eagles ta Najeriya wadda ke matsayin ta 6 a Afrika, sanya ta rukunin farko na nuna cewa za ta gujewa haduwa da kasashen Moroccon da Senegal mai rike da kambu kana Tunisia da Algeria da Masar.

Ivory Coast mai masaukin baki, wadda ta samu gurbi a gasar ba don kasancewarta mai masaukin baki ba, akwai yiwuwar ta hadu da Super Eagle ta Najeriyar ko da ya ke akwai fargabar kasashen biyu su ga junansu a rukuni guda da kasashe irinsu Kamaru da Mali da Burkina Faso baya ga Ghana da Jamhuriyyar demokradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.