Isa ga babban shafi

Jadawalin gasar cin kofin AFCON 2023 da zai gudana a Ivory Coast

Jadawalin hukumar kwallon kafar Afrika ya nuna cewa Senegal mai rike da kambun gasar cin kofin nahiyar za ta hadu da Kamaru a matakin rukuni yayin gasar wadda Ivory Coast za ta dauki nauyi a shekara mai zuwa.

Tawagar jami'an hukumar kwallon kafar Afrika yayin aikin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar na 2023 da zai gudana a Ivory Coast.
Tawagar jami'an hukumar kwallon kafar Afrika yayin aikin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar na 2023 da zai gudana a Ivory Coast. © RFI/Ndiassé SAMBE
Talla

A jiya Alhamis ne hukumar kwallon kafar Afrika ta fitar da jadawalin wasannin gasar a birnin Abidjan wanda ke sanya Senegal din a rukuni na C tare da makwabtanta kasashen Gambia da Guinea.

Dan wasan na Senegal kuma tsohon tauraron Liverpool da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya a yanzu Sadio Mane, na sahun ‘yan wasan da suka shiga aikin fitar da jadawalin, kuma a tsokacin sa bayan kammala rarraba kasashen a rukunnai 6 dauke da kasashe hurhudu kowanne ya ce ko shakka babu Senegal ta tsinci kanta a rukuni mai wahala amma za su yi iyakar kokarinsu wajen kai labari.

Morocco wadda ta kai wasan gab da na karshe a gasar cin kofin duniya bara a Qatar, wadda kuma za ta karbi bakoncin gasar ta cin kofin Afrika a 2025 a na ta rukunin za ta hadu da kasashen Congo da Zambia da kuma Tanzania.

A jawabinsa, bayan fitar da jadawalin dan wasan gaba na tawagar Moroccon da aka fi sani da Atlas Lions, Achraf Hakimi wanda shi ma ke sahun ‘yan wasan da suka yi aikin rarraba kasashen ya ce za su yi iyakar kokarinsu, kwatankwacin abin da suka yi a gasar cin kofin Duniya.  

Jadawalin ya nuna yadda Super Eagles ta Najeriya za ta hadu da mai masaukin baki Ivory Coast a matakin rukuni.

Tsohon tauraron Ivory Coast da ya taka leda da Chelsea kuma wanda ya taba lashe gwarzon shekara na Afrika har sau 2 Didier Drogba da kuma tauraron Najeriya Jon Mikel Obi da ya lashe kofin gasar ta cin kofin Afrika a 2013 na sahun wadanda suka yi aikin rarraba kasashen na Afrika zuwa rukunnai don tunkarar wasan na watan Janairu.

Ga dai yadda jadawalin ya ke

Rukunin A na kunshe da kasashen Ivory Coast da Najeriya sai Equatorial Guinea da Guinea-Bissau.

Rukunin B akwai kasashen Masar da Ghana da Cape Verde da kuma Mozambique.

Rukunin C akwai kasashen Senegal da Cameroon da kuma Guinea baya ga Gambia.

Rukunin D akwai Algeria da Burkina Faso sai kuma Mauritania da Angola.

Rukunin E na kunshe da kasashen Tunisia da Mali da Afrika ta kudu sannan Namibia.

Rukunin F kuma na karshe na dauke da kasashen Morocco sai jamhuriyyar Demokradiyyar Congo kana Zambia da Tanzania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.