Wasanni
Sadio Mane ya karbi lambar yabo matsayin zakaran Afrika na bana
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:02
Shirin Duniyar wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali ne kan bikin karrama zakaran kwallon Afrika da hukumar CAF ta yi a birnin Rabat na Morocco, kyautar da a wannan karon dan wasan gaba na Senegal da ke taka leda da Bayern Munich ta Jamus wato Sadio Mane ya lashe, wadda ke matsayin karo na 2 bayan lashe makamanciyar kyautar a 2019.