Isa ga babban shafi

Attajirin Qatar ya janye aniyar sayen kungiyar Manchester United

Hamshakin attajirin kasar Qatar Shiekh Jassim bin Hamad Al Thani ya janye shirinsa na sayen kungiyar Manchester United.

Filin wasa na Old Trafford da ke garin Manchester a Ingila.
Filin wasa na Old Trafford da ke garin Manchester a Ingila. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Attajirin ya yanke shawarar fasa sayen kungiyar ce, bayan da masu ita suka dage kan lallai sai dai ya biya euro biliyan 6 da suka nema, sabanin euro biliyan 5 da yayi tayin mika musu, tare da alkawarin biyan bashin da ake binsu na euro miliyan 970.

Tun bayan da a shekarar bara, Iyalan Glazer da suka mallaki United suka bayyana aniyar sayar da ita baki daya, ko kuma wani kason hannayen jarinta, Shiekh Jassim da attajirin Birtaniya Jim Ratcliffe ne suke kan gaba a tsakanin wadanda suka bayyana aniyar sayen kungiyar.

Sai dai bayan shafe tsawon lokaci ana kai kawo, aka fuskanci tsaiko kan tattaunawar, duk da kosawar magoya bayan Manchester United, wadanda suka fusata da iyalan Glazer, wadanda suka sayi kungiyar kan euro miliyan 790 tun a shekarar 2005.

A halin yanzu attajirin Birtaniya Jim Ratcliffe ake sa ran zai sayi kashi 25 cikin 100 na hannayen jarin United kan kimanin euro biliyan 1 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.