Isa ga babban shafi

Sancho zai koma Borussia Dortmund bayan gaza daidaitawa da Ten Hag

Dan wasan gaba na Manchester United Jadon Sancho na shirin koma tsohuwar kungiyarsa ta Borussia Dortmund da ke Jamus a matsayin aro cikin wannan kaka bayan bude kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu.

Tun cikin watan Satumban bara ake takun saka tsakanin Jadon Sancho da mai horarwa Erik Ten Hag.
Tun cikin watan Satumban bara ake takun saka tsakanin Jadon Sancho da mai horarwa Erik Ten Hag. © Sky Sports
Talla

Ana ci gaba da samun takun saka tsakanin Sancho da mai horarwa Erik ten Hag, bayan da dan wasan na Ingila mai shekaru 23 ya ki amincewa da bai wa mai horarwa hakuri game da wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Tun farko dai mai horarwa Erik ten Hag ya yi ikirarin cewa Sancho ne dalilin rashin nasarar Manchester United a wasansu da Arsenal cikin watan Satumban bara, batun da Sancho ya fito ya musanta kuma tun daga wancan lokaci ne dan wasan ya koma atisaye shi kadai kuma aka daina ganinsa a sahun ‘yan wasan da Ten Hag ke amfani da su.

A sakon da ya wallafa a wancan lokaci, Jadon Sancho wanda United ta sayo daga Borussia Dortmund cikin watan Yulin 2021 kan farashin fam miliyan 73 ya ce kawai Ten Hag na neman wanda zai fake da shi ne saboda tarin rashin nasarar da ya ke fuskanta.

Bayanai sun ce Borussia Dortmund a shirye ta ke ta karbi tsohon dan wasan nata cikin watan nan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.